Alkawari Hausa Novel

August 28th, 2022
ALKAWARI HAUSA NOVEL
ALKAWARI

Sauke cikakken littafin Alkawari Complete Hausa Novel. Wannan littafi zakuji dadinsa sosai. dan haka ga kadan daga cikin book din.

ALKAWARI HAUSA NOVEL

Dago fuskarsa yayi, wadda tuni hawaye sunyimata kawanya sannan yakara dacewa. Munyi iyakacin kokarinmu naganin mun ceci rayuwar wannan bawan Allah.

Amman babu yadda zamuyi Allah yariga ya yanke hukunci. Sai dai kawai aci gaba da yi masa addu’a Allah yajikansa kuma ya gafarta mai. Yana gama fadin maganarsa kawai yawuce gaba batareda yatsaya yin wani abuba.

Umma dake tsaye a gefenmu babu abinda ke fita daga bakinta sai. Inna lillahi wa’inna ilaihirraji’un. Yayinda khadija kau kuka kawai take rusawa abinta batama ko tinanin acikin mutane take.

Koda yaushe umma acikin tinanin rashin ahmad take. Munyi mata magana wannan tinanin zai iya haifar mata da matsala. Amman taki sauraren mu, sai abinda yayi gaba.

RELETED:  Abar So Hausa Novel

Bayan rasuwar ahmad da sati daya, inacikin daki sai naji karar khadija. Cikin sauri nafito domin inga abnda ke faruwa. Umma ce nagani kwance abakin kofa dasauri nakara sa na tambayi khadija lfy miya faru.

Ban tsaya jin amsa daga garetaba kawai nafita waje dasauri. Nasa mo mota bamu zame ko inaba sai asibiti. Batare da bata lokaci ba akashiga da ita domin duba lafiyar ta.

Mundauki kamar awa guda (1hour) zaune sai wata likita mace tafito. Cikin hanzari natashi na tarbeta tunkafin takaraso nake tambayarta. Doctor tana ina? Dagamin hannu tayi tana magana ahankali.

Ku kwantar da hankalinku munyi iya gwaje gwajenda zamuyi mungano cewa jininta ne ya hau. Saidai kuma faduwar datayi tasamu matsala a kashin bayanta.

Tana gama magana sai na tambayeta, likita yanxu miye abin yi. Batare da tabani amsa ba. Sai dai ta nunamin wani office tace in shiga likitan da zaiyimata aiki yana nan ciki.

Sauke cikakken littafin daga kasa

  • Format PDF
  • Last Updated May 21, 2021

CLICK HERE TO COMMENT

SHARE THIS ON

Be the first to comment

Leave a Reply