An kasa cika mana Alkawali Nayi wasti da Jam’iyyar ADP – inji Alan waka

January 5th, 2023

An kasa cika mana Alkawali Nayi wasti da Jam’iyyar ADP – inji Alan waka

Fitaccen mawakin nan Abubakar Aminu alan waka wanda ya fito takarar dan majalisa a karkashin jam’iyyar ADP wanda matashin dan siyasa Sha’aban Ibrahim shadara kamar yadda shafin freedom radio na ruwaito a shafinsu na sada zumunta inda wallafa kamar haka.

Ba za a yi takarar ba, an kasa cika mana alƙawari, kuma na yi watsi da jam’iyyar ADP nan take – Alan Waƙa

Mawaki Aminu Alan Waƙa ya fice daga jam’iyyar ADP ta Sha’aban Ibrahim Sharaɗa, sannan ya yi wurgi da takarar majalisar tarayya da yake yi a ƙaramar hukumar Nassarawa.

A cikin saƙon bidiyon da ya fitar, Ala ya nuna yayi danasanin fitowa ya bayyana kansa a matsayin ɗan takarar, domin ya ce babu wata takardar shaidar cewa yana takara da ya gani.

Ya kuma zargi ƙungiyar 13×13 da mawaƙi Dauda Kahutu Rarara ke jagoranta, wanda babban jigon ADP ne a Kano da yi musu an giza mai kantu ruwa kan shiga jami’yyar bisa sharaɗi.

Sai dai ya ce, daga baya ƙungiyar ta ƙasa yin kataɓis domin sanar da su matsayarsu, kurum an barsu da magana da wadanda ba su da hurumi.

Ala ya ce, tuni ya aike wa jami’yyar takardar sallama.

Meye ra’ayinku a kai?”

Hausaloaded.com ta bincike ta samu wanann Faifan bidiyo da alan waka ya wallafa a shafinsa na YouTube inda hausawa kance waka a bakin mai ita yafi dadi gashi nan sai ku saurara.


CLICK HERE TO COMMENT

SHARE THIS ON

Be the first to comment

Leave a Reply