Bakan Gizo Hausa Novel

August 22nd, 2022
BAKAN GIZO HAUSA NOVEL
BAKAN GIZO HAUSA NOVEL

Bakan Gizo Hausa Novel 

Bayan ta k’are ta d’an murza mai da powder sama sama ta fito d’akin. Tana shiga falon idanunta suka sauka akan fuskar Nasir dake zaune yana duba wasu takardu.

A hankali ta k’araso ta zauna a d’aya daga cikin kujerun dake falon. Duk da yaji takun zu wanta a palon amma bai d’ago kanshi ya kalleta ba.

Duba takardunsa kawai yakeyi har sai da ta cire girman kai ta kalle shi tace Barka da safiya. Ko kallo bata ishe sa ba ya kwashi takardunshi ya shigewar shi d’akin shi.

Amrah ta bishi da kallo ma i cike da mamaki tace Oh my god wai meke shirin faruwa da rayuwata ne?. Ba shiri wani sabon kuka yazo mata, a hankali ta fara sharar hawayen da ke ta ambaliya a cikin kwarmin idanunta.

Wata zuciya tace da ita taje taji meke da munshi, amman taji tsoron zuwa batasan abunda zai biyo baya ba a sanadin zuwan. Tana nan a zaune tana ta canki in cankar taje ko kar taje ne.

Sai gashi ya fito da shigar shi maikyau sai tashin k’amshi yakeyi, yana gyara zaman agogon hannunshi ne ya k’araso falon. Ba tareda ya kalleta ba yace.

Ni zan fita idan Adam yazo nema na ace ya sameni a majalisa. Yana kai k’arshen zancen shi ya fara taku zai bar falon, Amrah tayi k’arfin halin bud’a bakinta tace dashi A dawo lafiya.

Sauke cikakken littafin daga kasa 👇

  • Format PDF
  • Last Updated August 10, 2022

CLICK HERE TO COMMENT

SHARE THIS ON

Be the first to comment

Leave a Reply