Dan Sarkin Sauban Hausa Novel

August 29th, 2022
DAN SARKI SAUBAN
DAN SARKI SAUBAN

Download Dan Sarkin Sauban Hausa Novel written by Ummu safwan. Littafin yana dauke da shafuka Dari uku da casa’in. Dan nasan zakuj dadin sa.

DAN SARKI SAUBAN HAUSA NOVEL

Manyan motocine bak’ake guda biyar a jere da juna. Suna tafiya a kan lafiyayyen titi wanda yaji kwalta. Sai jiyaniya kakeji Tana tashi. Wanda motar jami’an tsaroce Suka rako yarima sauban domin Kula da lafiyarsa.

A katafaren wani babban gida Mai girman gaske mai d’auke da kwalliyar sarauta. A jikin gidan duk wanda yaga gidan yasan gidan sarauta ne. Dibo da yanayin gidan da kuma fadawan dake, gadin get din kofar gidan.

Idan ka diba ko wanne yana sanye da uniform dinsa blue tare da Dan sirkin ja a, jikinsu. Gidan adalin SARKI ne maiji da mulki da k’asaita.

Fadawa dake gadin get d’in k’ofar gidan zasu Kai kusan su a shirin ko wanne da abinda yake Kula dashi a wurin. Suna jiyo jiniya da sauri ko wannensu ya mik’e tsaye jiki na rawa Suka bud’e get.

RELETED: Sarkin Sarakai Hausa Novel

Sai murmushin farin ciki sukeyi, tare da dagawa motocin hannu cike da farin ciki. Sai da motocin Suka gama Shiga cikin gidan gaba d’aya snn, suka rufe get din. Suka runtuma su dukansu sukabi bayan motocin suna zubawa yarima Sauban kirari.

Jiniya tare da kid’e kid’e da bushe bushe ya karad’e gidan sarautar ga baki d’aya. Wanda duk wani halitta dake rayuwa a cikin gidan yasan yarima sauban ya iso mahaifarsa.

Da gudu sarkin gida ya Isa fada ya durk’usa a gaban maimarba sarki Abdullah ya Kai gaisuwa gareshi. Cike da girmamawa tare da yimasa Albishir na isowar yarima cikin k’oshin lafiya. Murmushi sarki yakeyi Yana girgiza kai.

Wanda duk Wanda ya kalli fuskar sarki kasan, yana cikin farin, ciki d’ansa Wanda yafi soyuwa a ransa ya, dawo, cikin k’oshin lafiya. Fadawa suka shiga cewa sarkin gida, sarki yaji dad’in wnn Albishir naka.

  • Format PDF
  • Last Updated June 27, 2021

CLICK HERE TO COMMENT

SHARE THIS ON

Be the first to comment

Leave a Reply