Duniya Biyu Mabambanta Hausa Novel

January 6th, 2023
DUNIYA BIYU MA BANBANTA HAUSA NOVEL
DUNIYA BIYU MA BANBANTA

Littafin Duniya Biyu Mabambanta complete Hausa Novel wanda ya samu rubutu daga marubuciya Maman shakur.

Duniya Biyu Mabambanta Hausa Novel

Sanye yake cikin kayan training na sojoji, a rantsettsiyar Base d’insu dake garin Bauchi. Wanda ko ina ka juya kalan shud’i kawai kake gani wato blue.

Matashi ne wanda ak’alla bazai gaza shekaru 34 a duniya ba, kallo d’aya zaka masa ka fahimci sam bashida jinin bak’in fata a tattare dashi, ma’ana duk yanda akayi wannan bawan Allah zama ce ta kawo k’asar bak’ak’e har ya koma d’an k’asa.

Wayace manne a kunnen sa na dama, basai ance maka answer waya yake ba. Daga looks d’in da yake dashi a fuskar sa zaka fahimce tsantsan tashin hankalin dake kwance saman fuskar sa.

Cikin nutsuwa da kwantar da hankalin mai sauraren nasa ya soma fad’in “Aunty Saudat kiyi hak’uri, nasan kinayi, da ace inada halin shigar da Yaya kotu da nayi, but kinsan yin hakan na nufin Innah ta min baki.

Aunty Saudat ina tsananin tausayin ki sannan ina gujema ranar da Fawaz zai dawo k’asar nan ya tarar da abinda akema mahaifiyar sa, bansan Yaya wani irin mutum bane amma kiyi hak’uri zanzo gidan ko gobe insha Allah kinji, Ki kwantar da hankalin ki.

Ya jima yana tsaye a wajen yana nazarin abubuwar dake faruwa A DUNIYAR SU har baisan sanda amini kuma k’ani a gareshi ya k’araso yanda yake ba wanda shima basai ance maka Sojan bane, shid’inma sanye yake cikin kayan training. Dogon saurayi wanda yarinta sosai ya nuna a fuskar sa, bazai wuce shekaru 25 ba duwa da shida.

Captain lafiya kayi tsaye a nan ka bar horas da rundunar naka.  cewan matashin Sojan saman da bai jima da k’arasowa wajen ba. D’an bud’e madaidaitan idanunsa yayi kafin yace.

Sauke Cikakken Littafin Daga Kasa


  • Format PDF
  • Last Updated April 28, 2021

CLICK HERE TO COMMENT

SHARE THIS ON

Be the first to comment

Leave a Reply