Kundin Kaddarata Hausa Novel

August 28th, 2022
KUNDIN KADDARATA HAUSA NOVEL DOWNLAOD
KUNDIN KADDARATA

Sauke Littafin  Kundin Kaddarata Complete Hausa Novel. Wanda yasamu Rubutu  daga marubuciya SAFIYYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA.

KUNDIN KADDARATA HAUSA NOVEL

Falo ne mai matsakaicin girma. Wanda ke dauke da set din kujeru labulaye carfet wanda dukkansu kalolin ash ne.  Turarre da kuma mai haske.  Daga bangare daya t.v plasma ce ‘yar matsakaiciya reciever da kuma D.V.D  wadanda aka qawata jeransu.

Can daga kowacce kusurwa ta falon, flower ce cikin plower vase dake a tsaye masu matsakaicin kudi. Sosai falon ya bada sha’awa duk da ba wani uban kudi aka narka masa ba. Saka makon yadda komai yake tsare a muhallinsa.

Bugu da qari kuma yadda ya wadatu da tsafta yake bada qamshin turaren wuta mai sanyi. Mamallakiyar falon ce zaune kan daya daga cikin kujerun falon. Matashiya ce wadda ba zata wuce shekara sha takwas ba.

Fara ce ba irin qal din nan ba. Tana da matsakaicin kyau. Wanda kwalliyar da tayi cikin shadda orange dinkin bubu ya sake fidda kyanta.

Dan kwalin shaddar na ajjiye gefanta, wanda ya zamo sanadiyyar bayyanar kitson dake kanta, qananu wadanda aqalla sun doshi guda dari da hamsin. Yadda falonta ke qamshi hakama jikinta yake yi.

A hankali ta daga kanta karo na barkatai ta sake aza su kan agogon bangon dake manne saman t.v plasma din dake gabanta maqale IP jikin bango. Sauke idanun nata tayi kana ta maida kan dan madaidaicin centre table din dake gabanta.

Ta miqa hannunta ta dauki wayarta samfurin tecno w3 ta sake lalubo lambar da tun dazun take ta nacin kira. Duk da cewa amsa daya ake bata tun dazun cewa lambar da take nema din a kashe take amma hakan bai sanyata ta daina kira ba.

Sauke Cikakken Littafin Daga Kasa

  • Format PDF
  • Last Updated April 23, 2021

CLICK HERE TO COMMENT

SHARE THIS ON

1 Comment

Leave a Reply