Mafarin Lamari Hausa Novel

September 9th, 2022

Shaharriyar marubuciyar zamani Zeeta ta rubuta mai suna Mafarin Lamari Hausa Novel. Zakuji dadin sa sosai gaskiya, dan haka ku garzaya kasa ku sauke shi.

Mafarin Lamari Hausa Novel

Cikin sanyin jiki Samir yajawo motar sa tare da barin k’ofar gidan. Wayar abokin sa Kabir yakira yake shaida masa cewar yaufa ya saki Sulty.

Wani ihu Kabir yasaki tare da cewa Like seriously abokina? shiru Samir yayi yakasa bashi amsa dan yana tunanin wannan farin cikin da Kabir yakeyi kuma na menene?

Hello! Samir kanajina kuwa, da gaske kasaki Aysher? Eh Kabir zanyi maka wasa ne da wannan zancen da ko a mafarki banyi tunanin faruwar shi ba. Kayi hak’uri abokina kad’auki hakan a matsayin jarrabawa.

Kai daga hutu ma ya sameka, karabu da jangwam, kaidai Allah baka wadda tafita kawai. Cewar Kabir. Samir yayi wani huci tare da fesar da iska mai zafi, kamar Kabir yana kallon sa yace Har’abadah bazan samu kamar Aysher ba.

RELETED: Bankada Hausa Novel

Da gaske nayi rashin da bazan ta6a mayarwa ba. Nidai fatana tasamu mu dai-daita kafin ta kammala iddar ta mu maida auren mu. Bari dai zankira ka idan nasauka zan wuce kaduna ina hanya.

Okay saika kira Allah tsare. Wani ihu Kabir yasaki, tare da cewa Alhamdulillahi yau burina yacika, zan samu gwarzuwan zuciyata. Shege harda wani cewa zaka maida ita kafin ta gama idda. Ai duk yadda yaza’ayi saina zuge ka baka mayar da ita ba.

Har sai tagama idda lokacin kuwa tazamo allura cikin ruwa. Barin harzarta zuwa na fara kaima mahaifinta gaisuwa. Yasan da zamana tun wuri. Zancen da Kabir yakeyi kenan shi kad’ai yana zaune a fine time restaurant.

Karasawa yayi gurin Isah, ya mik’a masa hannu sukayi musa baha. Kafin yafara gaishe da Isah, Isah ya amsa ba yabo babu fallasa, tun daga nan jikin Samir yafara yimasa sanyi. Dan da alama Aysher ta fasa kwan. Dan haka yace ma Isah Abokina dan Allah Baba yana nan kuwa?

Eh yana ciki Bismillah daman kai nake jira kazo na wuce gida, mushige daga ciki. Kai tsaye falon Baba suka shiga, bayan gaishe gaishe. Dakin yayi Shiru dan haka Samir yafara magana kansa a k’asa Baba nayi laifi ku gafarceni. Ku taimaka Aysher tadawo dakin ta, mu reni yaranmu ni da ita, dan Allah Baba.

  • Format PDF
  • Last Updated June 26, 2021

CLICK HERE TO COMMENT

SHARE THIS ON

About Author
Sarauta

I'm Muh'd Sarauta, one amongst the fellows behind the wheel ensuring you get the newest updates on Hausa EBooks. The founding father of ArewaFlex Media, also an Engineering student at Ahmadu Bello University, Zaria.

Be the first to comment

Leave a Reply