Saura Kwana 50 Numfashin APC Ya Ɗauke A Duniya

January 6th, 2023

Saura Kwana 50 Kacal Numfashin APC Ya Ɗauke A Duniya Saboda Aikata Lahira Jihadi Ne, Cewar Mustapha Inuwa

 

Daga Jamilu Dabawa, Katsina

 

Tsohan Sakataren Gwamnatin Jihar Katsina kuma Darakta Janar na yaƙin neman zaben Atiku da Lado a jihar Katsina, Alhaji Mustapha Muhammad Inuwa ya bayyana cewa tun daga ranar da dan takarar shugaban kasa a karkashin jam’iyyar PDP, Alhaji Atiku Abubakar ya gudanar da yaƙin neman zabensa a jihar Katsina, jam’iyyar PDP ta faɗa mawuyacin halin karkarwar zuwa lahira da shafe tarihinta a doran kasa kuma saura kwana hamsin kacal numfashinta ya dauke saboda aikata lahira jihadi ne, ta jefa al’ummar kasar nan cikin matsalolin rayuwa daban-daban.

 

Dakta Mustapha Muhammad Inuwa ya bayyana haka a wajen ƙaddammar da yaƙin neman zaben dan takarar gwamnan jihar Katsina a karkashin jam’iyyar PDP, Sanata Yakubu Lado Danmarke a karamar hukumar Funtua, jiya Laraba.

 

Darakta Janar na yaƙin neman zaben Atiku da Lado Danmarke ya kara da cewa ranar 25 ga watan Fabarairu, da za’a gudanar da zaben shugaban kasa da yan majalisar dattawa da na wakilai, ranar numfashin jam’iyyar APC zai kare a duniya, saboda daman yanzu a some take, ta na cikin makyarkyatar mutuwa, kuma da kyar za ta cika da imani ma saboda mawuyacin hali da ta jefa al’ummar Najeriya da jihar Katsina musamman halin rashin tsaro da tsadar kayayyakin masarufi.

 

Daga karshe, Dakta Mustapha Muhammad Inuwa ya miƙa godiya ta musamman ga duk wanda Allah ya ba ikon halartar ƙaddamar da gangamin kuma ya yi kira da al’umma su zaɓi nagartattun yan takarar da jam’iyyar PDP ta tsaida domin fitar da Najeriya da jihar Katsina cikin wannan bala’i da fitina da muke ciki.


CLICK HERE TO COMMENT

SHARE THIS ON

Be the first to comment

Leave a Reply