Takari Hausa Novel

September 14th, 2022

Sauke littafin Takari Cikakken littafin Takari Hausa Novel, wanda ya samu rubutowa daga marubuciya Zainab Idris Makawa. Littafin na dauke da shafuka dubu daya da hamsin da biyu, 1052.

TAKARI HAUSA NOVEL

Har muka kare hutun mu a makka Sheriff bai dawo ba daga tafiyan da yayi. Don yace daga Nigeria zai biya kasar Italy. Mun dawo madina lfy, munci gabada gudanar da karatun mu lafiya. Bamu da wani matsalar rayuwa yanzu don koda yaushe sheriff yana turo muna da kudi.

Duk da babu abinda muka rasa na rayuwa amma sai ya aiko muna da kudin nan. Salimat tasamu ciki mai wahal da ita sosai, don kusan duk abinda taci sai ta amayar da shi. Don haka yan zu kusan karatun mutum biyu nake yi. Inyi nata inyi nawa.

Sabo da gaskiya ba yabon kai ba wlh ina da gwargwa don ko karina sosai. Shiyasa koda nake hada aiki na da na Salimat, ba wai wani mugun wuya nake sha sosai ba. Dagani har Amal muna iya kokarin mu wurin kula da ita.

Saboda inkaga yadda ta koma sai ta baka tausayi sosai. Ganin irin wahalar da take sha, ne kuma gata gidan ita kadai ne aciki yasa mijin ta yabugo min waya. Cewa don Allah yana son mu taimaka mai salimat tadan dawo wurin mu ta zauna har taji dan sauki.

RELETED: Labarin Deebiza Complete

Saboda nasan cewa nima laba ni akayi sai, ban boye mai gaski ya ba nace zan bugawa sheriff. Yawa in fada mai idan ya amince zan fada mai saita dawo gidan namu. Sai da nafara yiwa Amal bayanin komai inda ita ma tace gaskiya Salimat tana bukatar taimako.

Don ita kadaice a gidan batare da kowa take zama ba.Tace min inwa sheriff magana ko zai yarda. Saida dare bayan na gama komai kuma na tabbatar cewa. Shima yanzu duk inda yake ya dan natsu. Watakila yana sama computer shima.

Sai nai dialing din noban shi. Zaune yake shida aziza a falon su na garin Riyadh, tayi dan filo da cinyan shi. Shiko yana aikin latsan system din shi, wayar shi tadan yi kara kadan. Bai dauka ba saida kiran ya kusa tsinkewa dakanshi.

Sanan yadiba yaga kowaye, Sunan fadima dayagani shi yabashi mamaki. Sai da yakara maimaita sunan san nan ya ansa sallama da nai mai cike da mamaki yake. Don dai gaskiya bantaba kiran shi a waya ba saidai shi din yakiramu yaji lafyan mu.

Saida na gama gashe shi sai kuma nadan shiru, jin shirun da nayi ne yasa shi yadan daga wayar nashi yadiba kona kashe ne sai yaga ina online.

  • Format PDF
  • Last Updated June 11, 2021

CLICK HERE TO COMMENT

SHARE THIS ON

About Author
Sarauta

I'm Muh'd Sarauta, one amongst the fellows behind the wheel ensuring you get the newest updates on Hausa EBooks. The founding father of ArewaFlex Media, also an Engineering student at Ahmadu Bello University, Zaria.

Be the first to comment

Leave a Reply