Zawarci Hausa Novel

August 21st, 2022
ZAWARCI hausa novel
ZAWARCI HAUSA NOVEL

Zawarci Hausa Novel

T are suka fito daga ɗaki farida da raihana Umma tana zaune a tsakar gida. Taihana tace Umma sai mun dawo. Umma tace to Allah yasa ku dawo lafiya ita dai umma bata san inda zasuje ba.

Amma raihana tace mata ganin marar lafiya zasuje. Suna fita daga gida suna tafiya kafin su isa wurin titi su samu abun hawa, duk inda suka wuce sai an nuna raihana.

Ga zawara uwar san banza ke wuta ƙaninki ɓarawo, dan a unguwar cewa suke ita a dole mai kuɗi take so bata aure sai mai kuɗi. Ita kuma raihana kwata kwata ba haka bane a wurin ta.

Amma mutane sai fassarata suke, wai ita ba kowan kowa ba galadiman kashi, ita ɗiyar talakawa amma baki aure sai gidan masu kuɗi. Lokacin da suka isa bakin hanya.

Sun ɗan dade sannan suka samu mai napep farida ta kwatanta inda za”a kaisu, saboda haka suka hau sai office in mai gida.

Lokacin da suka isa wurin aikinsu tun a bakin get in shiga. Kawayen mijin farida aka fara ah ah ah, madam yau da kanki. Farida saidai tayi murmushi, kafin su isa cikin office in mijinta har an mashi waya cewa ga madam nan zuwa.

Allah sarki sha”anin miji da mata sai Allah. Lokacin da suka shiga cikin office in cikin mutumci ya karɓe su. Sannan ya basu wurin zama.


CLICK HERE TO COMMENT

SHARE THIS ON

Be the first to comment

Leave a Reply